Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kotun koli ta tabbatar da Ahmed Lawan a matsayin dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa.
A hukuncin da kotun ta yanke, Mai shari’a Centus Nweze ta zargi Bashir Machina da shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta hanyar samo sammaci ba tare da shaidar baka ba da zata tabbatar da zargin da yake.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Bashir Machina shi ne ya lashe zaben fidda gwani da jam’iyyar APC ta gudanar,sai dai kuma jam’iyyar ta mika sunan Ahmad Lawan wanda ya shiga takar fidda gwani ta Shugaban kasa a jam’iyyar APC.

