2023: Samarin Kwankwasiyya sun Gudanar da addu’o’in samun Nasarar Zabe

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Kungiyar samarin kwankwasiyya dake unguwar marmara a karamar hukumar birni sun gudanar da taron addu’o’i domin samun nasarar yan takarar jam’iyyar NNPP daga sama har kasa a zabe mai zuwa .

 

Shugaban kungiyar Nasir Sani Sanda ya bayyana cewa sun gudanar da taronne domin neman Nasara ga daukacin yan takarar jamiyyar NNPP, na Karamar hukumar Birni da kewaye da Dr. Rabi’u Musa kwankwaso da injiniya Abba Kabir Yusif, domin cigaba da samar da ayyukan more rayuwa a fadin jihar nan.

Talla
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Shi ma anasa jawabin shugaban jam’iyyar NNPP na Karamar hukumar Birni Alh Hamza Bala, ya bayyana irin ayyukan cigaba da Gwamnatin kwankwasiyya ta samar a lokacin injiniya Rabiu Musa kwankwaso musamman a bangarorin ilimi da cigaban rayuwar al’umma.

 

Wani matashi Garzali Wali Marmara yace a shirye suke tsaf domin ganin a samu sauyin gwamnatin tun daga sama har kasa, duba da irin halin da al’umma suka tsinci kansu a karkashin gwamnatin APC.

 

Wakilinmu Kadaura24 ya bamu labarin cewa Taron ya samu halarta alumma da dama wadanda suka hadarda Alhaji Bashir Awu Rossi, Alh Bashir Usman Awu Rossi, da Alhajiji na goda, da Wakilin Ogan. Boye isyaku Musa da sauran jiga- jigan yan jamiyya NNPP na jihar kano.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...