Daga Abdullahi Danbala Gwarzo
A yau Alhamis ne wata mai gidan haya mai suna Temitope Olayiwola mai shekaru 45 da ta cire rufin gidan ƴan haya, ta gurfana a gaban wata babbar kotun majistare ta Sabo-Yaba da ke Legas.
Olayiwola da ke Plot na 15 a rukunin gidaje na Oyadiran, Sabo-Yaba, Legas, ta musa laifuka biyu da ake tuhumar ta da su na rashin zaman lafiya da lalata da gangan.
Mai gabatar da kara, SP. Thomas Nurudeen, ya shaida wa kotun cewa Olayiwola ta aikata laifin ne a ranar 10 ga watan Disamba, 2022, a Plot 15 Oyadiran Estate, Sabo-Yaba, Legas.

Ya yi zargin cewa Olayiwola da gangan ta cire rufin kwanon na Edem Yves da Evans Anyanwu, wadanda ke haya a gidanta.

Nurudeen ya bayyana cewa Olayiwola ta dauki matakin lalata rufin gidajen ne bayan da ta yi yunkurin biyansu kudin haya.
A cewarsa, laifukan sun ci karo da tanadin sashe na 168 da 350 na dokokin laifuka na jihar Legas, na 2015.
Alkalin kotun, Mista Peter Nwaka, ya amince da bayar da belin Olayiwola a kan kudi N600,000 tare da mutane uku da za su tsaya mata.
Bayan haka, ya dage sauraron karar har zuwa ranar 13 ga Maris, domin ci gaba da Shari’a.