A shirye muke mu cigaba da bada Shawarwarin da zasu inganta tsaro – Sarkin Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayato OFR ya bada tabbacin masarautar kano zata cigaba da bada hadin kai da goyon baya ga jami’an tsaro don kara inganta tsaro rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar kano da kasa baki daya.

 

Alhaji Aminu Ado Bayaro ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin sabon Kwamandan rundunar sojin sama na kano a fadarsa .

Talla

Sarkin ya bukaci sabon Kwamandan da ya zage damtse wajen ganin ya sauke nauyin da yake kansa, ta hanyar dorawa akan nasarorin da tsaffin kwamandojin rundunar da ya gada don inganta harkokin tsaro.

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

” A shirye muke mu baka shawarar da zata taimaka maka wajen inganta aiyukan ka, kawai duk abun da kake bukata don ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar kano da Nigeria baki daya”. A cewar Sarkin Kano

 

Sarkin ya ce ya ji dadi sosai kasancewar sabon Kwamandan rundunar sojin sama dan jihar Kano, Inda yace hakan zai sa ya kara dagewa don ganin jihar kano ta zauna lafiya ta hanayar yin aikin cikin gaskiya da rikon amana.

 

 

A nasa jawabin Sabon Kwamandan rundunar sojin sama na kano, Garba Ali Bello ya ce yaje fadar ne domin neman albarka da goyon bayan sarkin.

 

“Wajibi ne a gare ni na zo wanann fadar domin gabatar da akaina ga mai Martaba Sarki, sanann in bayyana masa irin shirin da na yi na bada tawa gudunmawar don inganta harkokin tsaro a jiha ta ta kano”. Garba Ali

 

 

Garba Ali ya baiwa Sarkin tabbacin zai yi duk mai yiyuwa don ganin jihar kano ta cigaba da zama lafiya, kuma ya bada tabbacin zai rika zuwa fadar domin neman shawarwari kasancewar Sarkin ya jima yana bada gudunmawa wajen inganta tsaro a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related