Wata uwa ta kashe aurenta ta auri saurayin ’yarta a Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

An fuskanci tirka-tirka a Karamar Hukumar Rano da ke Jihar Kano, lokacin da wata mata mai suna Malama Khadija ta kashe aurenta sannan ta auri saurayin ’yarta.

 

Lamarin ya faru ne bayan ’yar ta ta mai suna A’isha, ta ki amincewa da saurayin da ya zo neman aurenta, inda ita kuwa uwar ta ce ta ji ta gani, tun da dai Musulunci bai hana ba.

 

Talla

Tun da farko dai, ’yan uwan matar sun shaida wa gidan rediyon Freedom da ke Kano cewa suna zargin Kwamandan Hukumar Hizbah a Karamar Hukumar da aurar da ’yarsu ba tare da amincewarsu ba, inda suka ce ba su ma san inda take ba.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

To amma Khadija ta ce lafiyarta kalau, kuma tana zaune lafiya da sabon angonta lafiya.

 

Ta ce bayan ta gano ’yarta ba ta son mutumin, sai ta ce bai kamata duka su taru su yi asarar shi ba, inda ta tuntubi iyalinsa, inda ta ce ita ma kyakkyawa ce kamar diyar tata.

 

Khadija ta kuma ce, “Ba a jahilce na aikata haka ba. Sai da na tambayi malamai kuma suka tabbatar min da halaccin yin haka.

 

“Da na tambaye shi sai ya amince, amma iyayena da ’yan uwana suka ki daura auren. Dalilin ke nan da na yanke shawarar zuwa Hizbah, yanzu ga shi har mun yi aurenmu lafiya,” in ji ta.

 

Wani Kawun Khadija mai suna Abdullahi Musa Rano, ya ce da gangan suka ki amince mata ta auri sabon mijin tun da farko saboda suna zargin da gangan ta kashe aurenta na farko domin ta auri saurayin ’yar tata.

 

Ya ce, “Ta matsa wa tsohon mijinta lamba kan ya sake ta saboda ta auri wancan. Mu kuma muka ce ba za a yi wannan abin kunyar a danginmu ba, shi ya sa muka ki amincewa da bikin.

 

“Ba ma farin ciki da abin da Hizbah ta yi, kuma muna bayyana shi ne saboda mu kwato ’yarmu, muna so Babban Kwamandan Hizbah da Gwamnatin Jiha su saka baki a ciki,” in ji shi.

 

Sai dai da aka tuntubi Kwamandan na Hizbah a Karamar Hukumar, Ustaz Nura Rano, ya ce hedkwatar hukumar ta Jiha ce kawai take da hurumin yin magana a kan lamarin.

 

Shi ma da aka tuntube shi, Babban Kwamandan Hizbah na Kano, Sheikh Harun Ibn Sina, ya yi alkawarin bincika lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...