Bamu san adadin yan Nigeria da suka bata ba a hanyar ta zuwa cirani – Sadiya Faruq

Date:

Ministar Ma’aikatar jinkai da agajin gaggawa ta Najeriya Sadiya Umar-Farouk, ta ce babu wani takamaiman adadi mutanen da suka ɓata a Najeriya a hukumance, balle a dogara da shi a yi rijista.

Ta bayyana haka ne a Abuja ranar Talata a wani taron masu ruwa da tsaki wanda ma’aikatarta da hadin gwiwar Hukumar Red Cross suka shirta da kuma hukumar kare haƙƙin ɗan adam.

Talla

Sadiya wadda babban sakataren ma’aikatar Dr Nasiru Sani Gwarzo ya wakilta ya ce, a halin da ake ciki yanzu Najeriya ba ta tsari a hukumance domin tunkarar matsalar mutanen da suke ɓata a ƙasar.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Ta ce gwamnatin tarayya “ta damu kan yadda mutane ke wasa da taruwarsu saboda tafiye-tafiye”.

Tace tafiyar ciranin da ‘yan Najeriya ke yi, wadda ke haɗawa har da ƙananan yara domin tsallaka iyakokin kasar, ta sahara da tekun maliya domin samun rayuwa mai kyau a kowacce shekara, tana taimakawa wajen ɓacewar mutane.

Ta ƙara da cewa:”ƙididdigar da aka fitar da kwanan nan ta nuna cikin mutum 64,000 da suka ɓata a a nahiyar Afrika, 25,000 ‘yan Najeriya ne, kuma sama da 14,000 yara ne daga ciki.”

Shugaban ICRC a Najeriya Yann Bonzon, ya ce a kalla iyalai 13,000 a Najeriya na neman ‘yan uwansu da suka ɓata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...