Daga Rukayya Abdullahi Maida
Wasu ’yan uwa juna guda biyu, Abdullahi Rabi’u mai shekaru 17 da Musa Abdullahi, sun rasa rayukansu a wani bayan gida yayin da suka fada cikin shadda, a layin Abacha dake kasuwar sabon gari a karamar hukumar Fagge Kano.
Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne yayin da mutanen biyu suka yanke shawarar share ban dakunan dake da ke karkashin kulawar su domin yin amfani da su cikin tsafta.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya bayyana cewa, Musa ya fita daga hayyacinsa ne a lokacin da ya fada cikin masan , hakan tasa dan uwansa Rabi’u ya shiga ramin domin ya taimaka masa.

Ya kara da cewa, Musa da Rabi’u dukkansu ma’aikatane a gidan wankan l, sun mutu sakamakon zafi da rashin iskar oxygen kafin isowar ‘yan kwana-kwana.
Saminu Yusif ya bayyana cewa, jami’an hukumar kashe gobara ta jihar sun yi nasarar ceto su a sume, inda suka kai su asibitin musamman na Murtala Muhammad domin kula da lafiyarsu, daga bisani kuma likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.

“Mun sami kiran gaggawa da misalin karfe 08:41 na dare. Daga wani Nasir Muhammed cewa mutane biyu sun fada cikin masai .
Saminu ya kara da cewa, an mika gawarwakin wadanda abin ya shafa ga sufeto Abubakar Alhassan na sashin ‘yan sanda na Sabon Gari.