Daga Dija Aliyu
Shugaban kwalejin nazarin harkokin Addinin Musulunci da shari’a ta Aminu Kano, Farfesa Balarabe Abubakar Jakada, ya kaddamar da wani kwamiti da zai lura da irin tufa da dabi’un dalibai domin cusa tarbiyya a tsakanin daliban kwalejin.
Yace kwalejin ta haramta sanya suturar da ba ta dace ba, da kuma hana duk wata mota mai bakin gilas (tinted) shiga cikin Kwalegin.
Farfesa Balarabe ya kara da cewa, umarnin hana shiga da motoci masu bakin gilas ya shafi kowacce mota, Amma ban da motocin gwamnati.

Shugaban kwalejin ya bayyana cewa, daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu, 2023, duk motar da ba ta da lasisi, za a ajiye ta a wajen harabar Kwalejin.

Ya shawarci dalibai da jama’a, da su bi wannan sabon umarni, domin an kafa kwamitin ne don daukaka matsayin ilimi, da tabbatar da ingantaccen yanayin koyo, a Kwalegin .
Ya kara da cewa, kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Hajiya Rabi Ibrahim, yayin da Malam Nasiru Isma’il Minjibir zai zama sakataren kwamitin.
Kaddamar da kwamitin wanda ya gudana a dakin taro na Majidadin Kauran Katsina na Kwalejin, ya samu halartar dimbin masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.