Inganta tarbiyya: Makarantar Legal ta Kano ta haramtawa motocin dake da bakin gilas shiga cikin Kwalegin

Date:

Daga Dija Aliyu

Shugaban kwalejin nazarin harkokin Addinin Musulunci da shari’a ta Aminu Kano, Farfesa Balarabe Abubakar Jakada, ya kaddamar da wani kwamiti da zai lura da irin tufa da dabi’un dalibai  domin cusa tarbiyya a tsakanin daliban kwalejin.

 Yace kwalejin ta haramta sanya suturar da ba ta dace ba, da kuma hana duk wata mota mai bakin gilas (tinted) shiga cikin Kwalegin.
 Farfesa Balarabe ya kara da cewa, umarnin hana shiga da motoci masu bakin gilas ya shafi kowacce mota, Amma ban da motocin gwamnati.
Talla
 Shugaban kwalejin ya bayyana cewa, daga ranar Litinin 23 ga watan Janairu, 2023, duk motar da ba ta da lasisi, za a ajiye ta a wajen harabar Kwalejin.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
 Ya shawarci dalibai da jama’a, da su bi wannan sabon umarni, domin an kafa kwamitin ne don daukaka matsayin ilimi, da tabbatar da ingantaccen yanayin koyo, a Kwalegin .
 Ya kara da cewa, kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Hajiya Rabi Ibrahim, yayin da Malam Nasiru Isma’il Minjibir zai zama sakataren kwamitin.
 Kaddamar da kwamitin wanda ya gudana a dakin taro na Majidadin Kauran Katsina na Kwalejin, ya samu halartar dimbin masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku ba da gudunmawa kano ta zauna Lafiya – Waiya ya shawarci yan jaridun yanar gizo

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci kafafen yada labarai na...

KAROTA ta tabbatar da aniyarta na inganta matsayin jami’anta

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano...

Sarkin Sanusi ya amince da nadin sabon mai unguwar Hotoro GRA

  Mai martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi...