Gwamnatin Nijeriya ta ƙara farashin man fetur

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnatin Nijeriya ta ƙara farashin man fetur a hukumance da kashi 8.8, inda a halin yanzu farashin ya koma naira 185 daga 170.

 

Shugaban masu gidajen mai masu zaman kansu reshen Jihar Kano Bashir Danmallam ya tabbatar wa BBC da ƙarin inda ya ce sun samu umarni daga gwamnatin tarayya.

 

Talla

Sai dai dama tun kafin gwamnatin Najeriya ta yi wannan ƙarin farashin tuni wasu gidajen mai a Najeriya suke sayar da man a farashin da ya fi na hukuma.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Akwai masu sayarwa kan 190 har zuwa 350 a wasu jihohi da ke faɗin ƙasar.

 

Kafin yin wannan ƙarin, akwai gidajen mai da dama a fadin Najeriya waɗanda ba su iya sayar da mai saboda ƙarancinsa.

 

Ƙarin farashin dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ministar kuɗi ta Najeriya Zainab Ahmed ta tabbatar da cewa akwai yiwuwar a soma cire tallafin man fetur daga watan Afrilu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...