Ba mu taɓa tunanin ɗage zaɓen 2023 ba – INEC

Date:

Shugaban Hukumar Zaɓe a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya jaddada shirinsu na gudanar da babban zaɓe na 2023 a lokacin da aka tsara, yana mai cewa “ba mu taɓa tunanin ɗage zaɓen ba”.

 

INEC ta tsara gudanar da zaɓen daga ranar 25 ga watan Fabarairu mai zuwa, inda za a zaɓi shugaban ƙasa da ‘yan majalisar tarayya, daga baya kuma a zaɓi gwamnoni da ‘yan majalisar jiha a watan Maris.

Talla

Sai dai yayin wani taro a farkon makon nan, wani babban jami’in Inec ya bayyana cewa idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba matsalolin tsaro za su sa a ɗaga zaɓen a wasu yankunan Najeriya.

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

“Inec ba ta da wani tunanin sauya jadawalin zaɓen ballantana ma ɗage shi. Irin tabbacin da jami’an tsaro suka ba mu na tsaron lafiyar ma’aikatanmu ya ƙarfafa mana gwiwar ci gaba da shirye-shiryenmu,” in ji farfesan a ranar Laraba.

 

Ya ba da tabbacin ne yayin da ya gana da jam’iyyun siyasa 18 da za su fafata a zaɓen, inda ya gabatar musu da kundin rajistar masu kaɗa ƙuri’a da yawansu ya kai miliyan 93.4.

 

“Babban zaɓen 2023 zai gudana yadda muka tsara shi. Duk wani rahoton da ya ruwaito saɓanin haka ba matsayarmu ba ce,” kamar yadda ya jaddada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...