2023: Dalilin da ya sa muke aiki tare da manyan ƴan takarar shugabancin ƙasa na Najeriya – MDD

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yammacin Afirka da Sahel, UNOWAS, na hada kai da ƴan takarar shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki a Nijeriya domin tabbatar da zaben kasar cikin lumana.

 

Giovanie Biha, mataimakiyar wakilini na musamman na babban sakataren MDD kuma jami’in kula da harkokin hukumar ta UNOWAS, ta bayyana hakan a jiya Talata a birnin New York yayin da ta ke gabatar da sabon rahoton UNOWAS ɗin da ya kunshi abubuwan da suka faru cikin watanni shida da su ka gabata.

Talla

Biha ta ce ofishin ya kuma shaida rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin jam’iyyun siyasa a Najeriya domin inganta zabe cikin lumana.

 

“A jihar Kaduna, a watan Disamba 2022, Ofishin Jakadancin ya goyi bayan taron farko na masu ruwa da tsaki a matakin Jiha shida don inganta zabe cikin lumana. A jamhuriyar Benin, an gudanar da zaben ƴan majalisar dokokin kasar cikin kwanciyar hankali kwanaki biyu kacal da suka gabata,” inji ta.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

A cewarta, ko da yake yammacin Afirka da yankin Sahel na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro da ba a taɓa ganin irinsa ba, amma har yanzu “kasa ce mai dimbin damammaki”.

 

Jami’ar ta Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci jakadun da su ci gaba da ba da goyon baya ga dabarun da suka shafi karfafa juriya, inganta shugabanci nagari, da karfafa zaman lafiya da tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...