Daga Auwalu Alhassan Kademi
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da cewa jihar Kano za ta sake maimaita abin da ya faru a zaben shugaban kasa na 1993 da jihar ta goyi bayan dan takarar Kudu kuma ta ki zabar dan Kano a wancan lokacin.
“Hakan ya nuna girman siyasar ‘yan Kano, Mun zabi Cif MKO Abiola na jam’iyyar SDP kuma muka ki zabar Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC, domin dukkanmu mun yi imani da hadin kan kasa da kuma cancanta.” Ganduje ya jaddada

Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin rangadin yakin neman zabe tare da ’yan takarar jam’iyyar APC masu neman mukamai daban-daban a babban zabe mai zuwa, yayin da ya ziyarci Hakimin Kibiya, Alhaji Sunusi Abubakar Ila, bayan gudanar da taron yakin neman zabe da tuntuba a Rano da Bunkure wanda ya gudana a hedkwatar masarautar Rano.
Ya tunatar da ‘yan Nijeriya cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya goyi bayan ‘yan Arewa a lokuta daban-daban domin samun nasarar lashe zaben.

“Tinubu shi ya yi abun da yayi har jam’iyyar AC ta tsayar da Atiku Abubakar takarar shugaban kasa, sannan kuma ya tsayar da Nuhu Ribado takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ACN wadanda kuma dukkanin su yan Arewa .
Gwamna Ganduje ya jaddada cewa, Tinubu, daya tilo da ya cancanta kuma mafi cancantar cikin yan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, Arewa ce ke marawa masa baya, saboda imaninsa na ganin an gina kasa, Kuma ya gina yan adam sosai a matakai daban-daban .
Cikin sanarwar da babban Sakataren yada labaran gwamna Malam Abba Anwar ya gabatar da duk sauran ‘yan takarar da ke neman mukamin Sanata, dan majalisar wakilai da na jiha da na gwamna da na mataimakin gwamna na jam’iyyar APC.