Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kungiyar dalibai dake goyon bayan takarar gwamnan jihar kano a jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ta bada tallafi ga marayu dalibai a kananan hukumomin takwas na kwaryar birnin kano.
Da yake ganawa da wakilin Kadaura24 Shugaban kungiyar Alhaji Ali Ali ya ce sun bayar da tallafin ne domin fitar da dalibai marayu daga cikin mawuyacin hali.

” A kokarin mu na ganin mun taimaka dan takarar mu na gwamna wajen gudanar da irin aiyukan da ya Saba yi na hidimtawa marayu don inganta harkokin karatun su da rayuwar su baki daya”. Inji Ali Ali
Yace tallafin zai taimaka wajen magance matsalolin da Marayu suke fuskanta, saboda iyayen su maza da suke daukar dawainiyar su sun koma ga Allah, kuma su matan abubuwan neman me zasu ciyar da marayun sun yi musu yawa.

kayiyakin da aka raba sun hadar da jakar makaranta da litattafan karatu da biro, Uniform din makaranta da dai sauransu.
“Su kuma iyayen marayun dake kananan hukumomi 8 na birnin kano, mun basu tallafin taliya da shinkafa domin rage musu radadin halin da suke Jakar makaranta da litattafan karatu da biro
Uniform din makaranta dukka ga marayu fadin local govt 8 na cikin birni”. Inji Ali Ali