Daga Halima Musa Sabaru
•Ya kuma goyi bayan takarar shugaban kasa na Atiku.
Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Sanata Jibrilla Bindow yasa kafa ya fice daga APC zuwa Jam’iyyar PDP kuma ya bada tabbacin goyowa Gwamna Umaru Fintiri baya a takarar da yake sake yi.
Tsohon gwamnan wanda tsohon dan jam’iyyar APC ne ya bayyana haka ga gwamna Fintiri ta karkashin shugabannin kungiyoyi magoya bayan sa har guda 250.

Da yake jawabi a dakin taro na Banquet dake gidan gwamnati Yola a ranar Litinin, shugaban tawagar Abdullahi Bakari ya ce sun kai ziyarar ne bisa umarnin shugaban jagoran su tsohon gwamna bindow.

A cewar jagoran, tsohon gwamnan ya bukace su da su mika godiyar sa ga gwamna Fintiri sakamakon kammala ayyukan da ya gada a fadin jihar.
Sun kuma yi alkawarin bada gudunmawa ga takarar shugaban kasa ta tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, wanda a cewarsu ya kasance jagoransu tsawon shekaru don haka yana bukatar goyon bayansu ga takararsa ta shugaban kasa.