Yadda gwamnatin jihar kano ta Magance Matsalar Rashin Tsaro a Makarantun Gwamnati

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida
A bayyane yake halin da makarantun gwamnti  suke ciki  a wasu shekarun baya ta fuskar barazanar rashin tsaro daga bata-garin da suke maida makarantun guraren da suke cin karensu babu babbaka, saboda fahimtar da su ka yi cewa babu mai iya tanka musu.
Idan ma suka ga dama basa fita daga makarantun har sai lokacin da suka ga damar fita sannan mu kuma mu share namu faggen na koyawa yara ilmi, Kuma ba wani abune ya haifar da hakan ba illa rashin katange makarantun don basu tsaron da ya dace.
Talla
Shugaban wata makarantar sakandire da take fuskantar irin wannan kalubale yace kafin zuwan sabon tsarin da gwamnati mai ci ta fito da shi, makarantu  sun fuskanci kakubale musamman makarantun cikin kwayar birni da kewaye.
Manyan kalubalolin da makarantun gwamnati suka fi fuskanta a bangaran ilmi musamman a wadancan lokuta da suka shude sune batun rashin cikakken  tsaro a makarantun ta yadda binkice ya tabbatar da cewa wasu daga cikin makarantun sun tasamma zama matattarar aikata manyan laifuka, tun daga kan fatauci da sha da sayar da miyagun kwayoyi  da Kuma uwa  uba boye makaman da ake fita ayi ta’adanci dasu.
Wani bangare na yadda makarantun suke
Galibin irin wadanda abubuwa kan faru har a lokutan da dalibai ke haramar shiga ajujuwa domin daukar karatu, inda a kan yi rashin sa’ar iske irin wadancan bata gari suna kokarin  fitowa daga ajujuwa yayin da  wasu ke dirowa daga rufin dakunan ajujuwan  domin fita ayyukansu na ta’adanci.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
 
 Wadannan mugwayen halaye da  dabi’u su suka jawo ra’ayin wasu daga cikin iyayen na cire ya’yansu kaco-Kan daga makarantun gwamnati  saboda fargabar abubuwan da kanje su zo, ta yadda lamarin kai tsaye  ya ke  shafar ilmin wasu daga cikin daliban da iyayensu ke daukar wancan mataki  Maza da Mata baya ga daliban dake kokarin shiga babbar makarantar sakandire wadanda suma lamarin ke shafa.
 Binkicen da jaridar Solace Base ta gudnar ya nuna cewa makarantun da ke fuskantar wadannan kalubale sun hada da babbar makarantar sakandiren gwamnati ta Stadium dake titin Airport da sakandiren yan mata ta Dabo dake Kan titin France Road, da sakandiren yan Mata ta  Kwachiri da ta Chiranci da sauran makarantun dake yankin cikin Birnin Kano .
Yadda aka fara wasu makarantun bayan fara shirin PPP
Sai dai a dai-dai lokacin da lamarin yayi karfin da  yake nema yafi karfin kowa kwatsam sai gwamnatin Kano tayi wani karatun ta nutsu, ta hanyar bullo da wani shirin hadin gwiwa da wasu bangarori masu zaman kansu ta yadda za’a samar wa wadancan makarantu mafita daga halin da suka tsinci kansu na rashin cikakken tsaro.
An bijiro da shirin ne karkashin shawarwari da bukatun neman yin hakan daga bangaran makarantun da suka fi fuskantar matsaloli rashin tsaro saboda bata-garin da suka addabesu da shaye-shaye da sauran laifuka, kamar da yadda  wasu daga cikin jami’an kula da tsare-tsaren gyaran makarantun gwamnatin jihar Kano suka bayyana.
Shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin da bangarori masu zaman kansu da aka yiwa lakabi da (PPP ) shiri ne da gwamnatin kano tace ta samar dashi ne domin samar da ishashen tsaro ga makarantun gwamnati tare basu kulawa ta musamman abangaran gudanarwa da kuma  cimma nasarar shirin gwamnatin Kano na bada Ilimi kyauta kuma dole.
 An kuma dora alhakin kula da shirin ga wasu bangarorin gwamnati domin aywatar dashi.
Bangarorin kuwa sun Hadar da hukumar raya Birane ta jihar Kano (KNUPDA) da Majalisar dokoki ta jiha, da Kwamitin Gudanar da Makarantu na jihar Kano (SBMC) da  kuma Kungiyar Iyaye da Malamai wato (PTA).
 Tuni dai Masana lamuran yau da kullum ke kallan tsarin a matsayin hanyar da zata taimaka wajen magance kalubalen da ke tattare da karancin koyo da koyarwa a makarantun, harma da mangance barazanar rashin  tsaron da makarantun ke fuskanta.
Sai dai wasu daga cikin masu tsokaci kan lamuran yau da kullum suna kallan lamarin a matsayin nakasu a bangaran kwazon dalibai musamman duba da cewa galibin makarantun da tsarin zai shafa, makarantu ne da za’a gine su da shaguna wanda haka suna ganin ka iya shafarwabharkokin karatun matsala saboda matse makarantu da za’a rikayi da shaguna a lokuta daban-daban.
Sai dai cikin martanin da ya mayar Shugaban hukumar tsara  Birane ta jihar Kano KNUPDA, Arch. Sulaiman Ahmad Abdulwahab, ya ce “Haryanzu Al’umma da dama basu gama fahimtar Alkhairan da shirin zai haifar ga cigaban ilmi a jihar Kano ba.
Yace ayyukan kewaye wasu daga cikin makarantun da suke fuskantar matsalar tsaro, ayyuka ne da ke gudana karkashin wannan shiri ta yadda makarantun zasu sami cikakken tsaro, saboda shagunan da ke kewaye dasu, baya ga samun cikakkiyar kulawa a  bangaran gudanar da makarantun yadda ya kamata.
 ” A yanzu haka ma maganar da ake tuni muka cimma matsayar fara gudanar da ayyukan gyaran wasu daga cikin makarantu gwamnatin Kano karkashin wannan shiri na PPP, domin shiri ne na hadin gwiwa da wasu bangarori masu zaman kansu domin samun hanyoyin kula da makarantu da basu tsaro da kuma samun isassun kudaden gudanar dasu”. Inji MD KNUPDA
 ” Yanzu haka mun yi nasarar tantance makarantu guda 21 mallakin gwamnatin jihar Kano wadanda zamu fara wannan aiki. Sai dai dukkanin abubuwan da muke fatan cimma nasara zasu tabbata ne gwargwadan hadin gwiwar da kuma goyan bayan jama’a, saboda haka muna rokon Al’umma da su fahimci shirin sosai saboda muhimmancinsa wajen inganta  sha’anin Ilimi a Kano”  inji MD KNUPDA.
Arch Suleiman Ahmad ya kara da cewa “A yanzu haka ma hukuma tana  nazarin neman hadin gwiwar majalisar dokokin Kano kan gyaran dokar kula da lamuran da suka shafi abubuwan da ake gudanarwa na sana’a a kewayen makarantu ta yadda gwamnati za ta samu hurumi sosai a bangaran gudanar da lamura a kewayen makarantu.
 A ziyarar baya bayan nan da ya kai wasu daga cikin makarantun da lamarin ya fi shafa, shugaban hukumar tsara birane ta jihar Kano Arch Suleiman Ahmad  ya bayyana cewa sama da kashi 85% na ayyukan gyaran makarantun guda takwas kashi na farko ya kammala, da suka hada da babbar makarantar sakandiren G.S.S, Stadium da makarantar sakandiren Mata  ta G.G.S.S.S Dabo, sai babbar makarantar sakandiren G.S.S Kwakwachi  da babbanr sakandiren Bachirawa, da sakandiren  Kofar Nasarawa, da sakandiren Yan mata dake  Dukawuya, da sakandiren  Goron Dutse, da sakandiren yan Mata  ta Chiranchi da kuma makarantar Firamare dake  Chiranci.
 Shugaban kwamitin gudanar da makarantun ( SBMC ) na makantar sakandiren gwamnati ta Stadium Alhaji Muhammad Lawal, ya ce sun kwashe sama da shekaru shida suna rubuta koke-koke  ga gwamnatin jihar Kano kan lalacewar kayayyakin koyo da koyarwa  da matsalar rashin tsaro da ta addabi makarantar, Amma daukar matakin ya gagara.
 “Mun dade muna cikin wannan hali kafin zuwan wannan shiri na kula da makarantu, gashi shi yanzu shirin ya taimaka wajen katange mana makaranta da gina karin sabbin Ajujuwa bakwai ( 7) da bandakuna goma sha biyar (15)  da Kuma gyara dakunan gwajegwajen  makarantar ” Inji Muhammad.
 Haka lamarin yake a bangaran makarantar sakandiren Yan mata ta Dabo dake kan titin France Road Kano, shugabar makarantar Hajiya Binta Abdulhamid, ta ce babban kalubalen da ya addabi makarantar a wancan lokaci shi ne batun barazanar tsaro daga masu shaye-shayen dake haurowa makarantar daga unguwar Sabongari saboda kusancin makarantar da Unguwar.
 “Gaskiya rashin katanga a makarantar ya taimaka wajen shigowar bata-garin su ke haurowa makarantar cikin sauki tare da sace kayayyakin makarantar bayan sun yi shaye-shaye a makarantar.
” Don haka suke samun damar  haurowa su saci kayan makarantar yi sata da lalata mana dukiya. Wani lokaci sukan shiga ofis ta silin su aikata barna da ta’adanci”. Inji Hajiya Binta
Saboda haka a shekarar 2015 muka yi taron hadin gwiwa na PTA na makarantu a Sabon Gari tare da mika kokenmu ga gwamna” .
 Hajiya Binta ta kara da cewa  “Mun ba da shawarar gina shaguna a katangun makarantun da suke da irin wannan matsalar, saboda samar da shagunan zai Samar da tsaro saboda masu shagunan za su hada kai da jami’an tsaro domin kare dukiyoyinsu.
 Tabbas wannan shiri ya taimaka wajen ragewa gwamnati nauye- nauye.
Domin kuwa mun  gina katangu guda biyu , da bandakuna goma (10) da sauran gyare gyaren makaranta.
Shima Shugaban makarantar sakandire gwamnti ta G.S.S Kwakwachi, Malam Auwalu Ado, ya ce makarantar da aka kafa a shekarar 1983 ba a taba ganin wani gyara da ya kai ga rushewar gine-gine da rufin ajujuwa ba.
Ya ce katangar makarantar ta dade da lalacewa saboda yawan ambaliyar da  rafin dake gefen makarantar ke yawan yi.
 “Rushewar katangar ya sa mu fuskantar muminar  barazanar tsaro daga Yan daba da masu shaye shaye wadanda galibi suka mamaye makarantar domin sace rufin rufin kwano da tagogi da kofofi da sauran kayayyakin makaranta.” in ji shi.
 Ado ya ce “Mun mika rubutacciyar makarantar  kwamitin SBMC da PTA da kuma gudanarwa sun fara rubuta wasikun korafe-korafe tun a shekarar 2007 tare da yin kira da a gyara. Kafin daga baya  su tuntubi hukumar tsara Birane ta jihar Kano KNUPDA kan halin da makarantar ke ciki Inda abin mamaki a halin yanzu hukumar  na gudanar da aikin gyaran makarantar ka-in da na-in “.
 Hakazalika, shugaban kwamitin gudanar da makarantu na babbar sakadiren gwamnti  ta G.S.S Kofar Nasarawa,  Malam Habibu Dauda Yakasai, a lokacin da yake yabawa shirin ya ce abun a yaba wa hukumar tsara Birane ta jihar Kano KNUPDA ne saboda  ta gyara ajujuwa guda  shida a makarantar, ta gina bandakunan dalibai shida da bandakunan ma’aikata biyu don magance matsalar karancin ajujuwa da Kuma kauda matsalar tsuguno a guraren da basu dace ba.
 A nasa bangaren, daraktan tsara gine-gine na hukumar KNUPDA, wanda shi ne shugaban kwamitin na jihar Kano , Arch.  Salisu Bello, ya ce an cimma kusan kashi 90 cikin 100  a matakin farko aikin gyaran makarantun da suke da manyan matsaloli.
Yace makarantu goma sha biyu ne 12 wadanda ake saran kammala su a kashi na biyu na shirin.
 Salisu ya ce ana gudanar da gyare-gyaren ne tare da amincewar hukumomin makarantun domin a tabbatar da cewa aikin da aka yi ya yi dai-dai yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...