‘Yan sanda sun kashe masu safarar makamai biyu a Zamfara

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce jami’anta sun kashe wasu masu safarar makamai biyu a kan hanyar Gummi zuwa Anka.

Bayan sun yi musayar wuta na kusan sa’o’i da masu safarar makaman, waɗanda ake zargin sun ɗauko makaman tun daga jihar Taraba domin kai su sansanin ‘yan ta’adda a Zamfara.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Mohammed Shehu Anipr, ya sanya wa hannu, ya ce lamarin ya faru ne bayan da jami’an nasu suka samu bayanan sirri game d

Talla

a mutanen waɗanda ke cikin ƙaramar mota ƙirar ‘Toyota Corolla’ ɗauke da muggan makamai domin kai su sansanin ‘yan ta’adda a jihar.

Bayan musayar wutar ‘yan sandan sun kama mutum biyu waɗanda suka ji munanan raunuka yayin da wasu suka tsere da raunkan harbi a jikinsu.
An kai mutanen biyu asibiti inda daga baya likita ya tabbatar da cewa sun mutu bayan an kwantar da su a asibitin.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Daga cikin abubuwan da ‘yan sandan suka ƙwato sun haɗar da ƙaramar mota kirar Toyota Corolla, da harsasan manyan bindigogin harba gurneti uku, da abubuwan fashewa uku, da harsasan bindiga ƙirar AK47 151, da harsasan makamin harbo jirgin sama 200, da wasu layu da guraye.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Kolo Yusuf ya sake jadadda burin rundunar na fatattakar ‘yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka daga jihar, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...