Daga Umar Sani Kofar Na’isa
Wani dan takarar majalisar wakilai a kananan hukumomin birnin Kebbi Kalgo da Bunza dake jihar Kebbi a jam’iyyar PDP Barr. Abba Bello Muhd ya rasu yana shirin fara fita yakin nema zaben kujerar da yake nema.
Dan takarar ya rasune a babban birnin tarayya Abuja bayan ‘yar gajeriyar jinya, ya rasu ne ya ana da shekaru 42 yana da mata daya da ‘yarsa guda daya.

Marigayi Barr. Abba Bello da ne ga tsohon Minista tsaro, kuma tsohon Ministan sadarwa na Nigeria Kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa Dr. Bello Halliru .
Kafin rasuwar sa a daren jiya juma’a shi ne wanda jam’iyyar PDP ta tsayar takarar Dan majalisar tarayya ya yankin Birnin Kebbi Kalgo da Bunza, ya kuma taba neman kujerar a shekara 2015 Amma Allah bai bashi nasara ba.

Rahotannin da kadaura24 ta samun sun nuna za dai ayi jana’izarsa a babban masallacin Abuja da misalin karfe 1 na ranar wannan Asabar din.