Daga Rahama Umar Kwaru
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce jihar Borno na da ingantaccen tsaro za a iya gudanar da zabukan 2023.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yau Juma’a yayin ziyara ga shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

BBC Hausa ta rawaito Gwamna zulum ya tabbatar wa masu ‘yan jihar cewa za a basu cikakkiyar tsaro kafin da lokaci da kuma bayan zaɓe.
A baya-bayan nan ne ake nuna fargaba kan tsaro a jihar bayan da aka kai wa tawagar ƴakin neman zaɓen shugaban kasa na jam’iyyar PDP hari a Maiduguri a ranar 22 ga watan Nuwamba.

”Muna iyakar bakin kokarin mu a yanzu, muna shirye-shiryen sake mayar da mutane garuruwansu da kuma ganin yadda za mu sake gyara hanyar Maiduguri da Gamborun-Gala da kuma ta Maiduguri zuwa Banke da zimmar ganin mutane sun koma rayuwa kamar a baya,” in ji Gwamnan.