Alan waka ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam’iyyar Sha’aban Sharada Sharada

Date:

Daga Abdulhamid Durimin Iya

 

Fitaccen mawakin nan Aminudden Ladan Abubakar wanda aka sani da Alan Waka yace rashin tabbas ne yasa ya ajiye takarar sa kuma ya fice daga jam’iyyar ADP ta Sha’aban Sharada.

 

Alan waka ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24 yau asabar .

 

Yace dama gayyatar sa akai cikin jam’iyyar kuma akai masa alkawarin za’a bashi takarar dan takarar tarayya a karamar hukumar Nasarawa, amma bayan ya fara harkokin takarar gadan-gadan kuma hukumar zabe ta fitar da sunayen yan takara kuma ya ga babu sunan shi.

Talla

 

” A sunayen yan takara da INEC ta fitar babu sunana, kuma babu wani cikin shugabannin jam’iyyar ko jagororin ta da ya yi min gamshen bayani game da halin da ake ciki da Kuma matsayin takarar, an ajiye ne kamar allo, hakan tasa na yanke shawarar barin jam’iyyar”. Inji Alan waka

 

Aminu Ala ya kara da cewa ya fahimci idan ya cigaba da zama a jam’iyyar a matsayin dan takarar zasu iya karewa a kotu da wanda hukumar zabe ta sanya sunansa a matsayin wanda ta Sani yana takarar dan majalisar tarayya a jam’iyyar a karamar hukumar Nasarawa.

 

Talla

Game da batun ganin da aka yi musu da mataimakin gwamnan kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ala yace dama Gawuna yayansa ne duk da yake basu taba irin Zaman da sukai jiya ba.

 

  • ” Bayan ficewata daga ADP yan siyasa daga sassa daban-daban sun neme ni, mataimakin gwamnan shi ma ya gayyace ni kuma na je kamar yadda kowa ya gani, amma dai idan lokacin yayi kowa zai ji yadda ake ciki, kuma dama hausawa suna cewa idan kaga kare yana shinshina takalmi to dauke zai yi”. Inji Alan waka

 

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Aminu Ala yana daga cikin yan Kannywood da suka shi ga jam’iyyar ADP bisa jagorancin Dauda Kahutu Rarara Kuma har aka baiwa wasu daga cikin su takara, amma dai a sunayen da hukumar zabe ta fitar na yan takara babu sunan kowanne daga cikin su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...