Daga Nura Abubakar Cele
Dan takarar majalisar tarayya na kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam a jam’iyyar APC Hon Dr Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce duk kalaman tunzuri da aka ce Shugaban jam’iyyar APC na kano Hon. Abdullahi Abbas yana yi wajen Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya koya.
Kadaura24 ta rawaito Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wata hira da akai da shi a rediyo Mai taken “Matakin Nasara 2023” wanda ake sakawa a gidajen radio dake Kano.
Musa Iliyasu yace Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso duk Kano yafi kowa yin kalaman da suke tunzura al’umma musamman matasa, Inda ya ce ai a wajen Kwankwaso Abdullahi Abbas ya koyi irin wadannan nan kalamai.

” Kwankwaso da yan kwankwasiyya su suke kalaman na tunzura al’umma, don haka yaren da suke ganewa kenan, shi kuma Abdullahi Abbas yafi kowa iya yaren don haka yake yi musu magana da yaren da suka fi ganewa”. Inji Musa Iliyasu
Musa Iliyasu dai yana martani ne ga dan takarar gwamnan Kano na Jam’iyyar NNPP Engr. Abba Kabir Yusuf bisa karar da yakai yana neman kotu ta tilastawa kwamishinan ‘yan sandan don ya binciki Abdullahi Abbas, Yace suma yanzu haka suna hada bayanai da zasu Kai Kwankwaso Kara akan kalaman da ya rika yi.

” Yanzu haka a wayata Ina da maganganu na tunzura al’umma da Kwankwaso ya Rika amfani da su a yayin yakin neman zabe, hakan tasa Shugaban jam’iyyar mu tunda sun zauna tare ya koya sai yake yi musu magana da yaren su”.
“Idan kai ( Abba Gida-gida) ka kasa gano kalaman da Kwankwaso yake yi ba dai-dai bane, to mu ma yanzu lauyoyin mu suna chan suna hada bayanai zamu maka Mai gidanka a gaban kotu tunda Muna da hujjoji sun fi 100 na irin wannan kalamai” . Inji Musa Iliyasu Kwankwaso