Daga Sani Danbala Gwarzo
Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello matawallen muradun yace talaka ba abin yadawa bane, kamata yayi masu rike da madafan iko su maida hankali wajen rungumar al’ummar sun domin jin irin matsalolin da su ke damunsu.
Gwamnan matawalle ya bayyana hakan ne a yayin taron bude babban ofishin kungiyar G7 business community dake kan titin zoo Road, wanda ‘yan kungiyar da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jamiyar APC a jihar suka samar.
- “Ba zaka San matsalolin mutane ba dole sai ka matsa kusa da su , hakan ne zai baka damar sannin matsalar da Kuma hanyoyin da zaka bi don magance matsalolin”. Inji matawalle

Gwamnan ya buƙaci yan kungiyar da su yi aiki tukuru don ganin jam’iyyar APC ta yi nasara a zabukan dake tafe, domin samun damar cigaba da hidimtawa al’ummar jihar kamar yadda gwamnatin sa ta faro.
” Babu shakka kunyi namijin kokari wajen samar da wannan ofishin da Kuma yadda kuke yada manufofin jam’iyyar APC tun daga shigowarku, Babu shakka akwai bukatar sauran kungiyoyin su yi koyi da aiyukan ku don samun nasarar mu baki daya”. Inji gwamna matawalle

Shi kuwa a nasa jawabin babban daraktan kungiyar G7 Hon. Ibrahim Khalil Ahmad ya ce babu abinda ya ja ra’ayin su game da komawar su jam’iyyar APC face karamci da gwamna zamfaran yake nunawa al’umma baki daya.
- “Hakan ta sa muka canza shekar daga waccan jam’iyyar ta PDP zuwa jam’iyyar mu ta APC mai albarka kuma babu gidan da muka sauka sai gidan Mai darajar matawalle saboda mutum ta dan Adam”.inji Hon. Ibrahim Khalil
Daraktan kungiyar ya yi alkawarin cigaba da tallata manufofin gwamna matawalle da na jam’iyyar APC baki daya a jihar Zamfara da kasa baki daya.