Daga Auwalu Alhassan Kademi
Hukumar Jin dadin alhazai ta jihar kano tace ta kammala dukkanin wasu shirye-shirye domin fara bitar alhazai tsakiyar wannan wata na Janairu don tunkarar ibadar aikin hajjin bana.
Sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Muhammad Abba Danbatta shi ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a ofishinsa.
Muhammad Abba yace sun fara shirin ne tun yanzu saboda akwai sabbin cigaba da aka samu tun daga kasar saudiyya har zuwa hukumar aikin hajji ta kasa Nahcon dama tasu hukumar. Yace a bana saudiyya ta Kara yawan adadin alhazai a Nigeria fiye da na shekaru 3 da suka gabata.

“Bana karamar yadda aka Sani an baiwa Nigeria kujerun alhazai Dubu 95 kamar yadda aka bayar a shekara ta 2018 da 2019, don haka muna sa ran zamu kwashe dukkanin alhazan mu, wadanda suka rage da ma wadanda zasu biya a bana”.inji Danbatta
Yace kasar saudiyya ta cire aune-aune cutar Corona da ake na musamman na awanni 72 kafin tashi zuwa kasar, kawai a bana abun da ake bukata shi ne shaidar kammala allurar corona, hakan tasa tuni muka shirya yin sauran gwaje-gwaje a asibitin hukumar dake sansanin alhazai.
Babban sakataren ya kuma Kara da cewa a bana kasar saudiyya ta cire dokar hana wadanda suka haura shekaru 65 zuwa aikin hajji, sannan yace suna cigaba da biyan alhazan badi ragowar kudaden su da aka dawo da su kaga saudiyya sakamakon gaza gudanar da wasu hidimomi ga alhazai.

“Hukumomi a kasar saudiyya sun samar da karin tashoshin jirage guda biyu a madina, sannan Kuma Muna kira ga wadanda suka bar kudaden su musamma wadanda aka yiwa biza da su hanzarta zuwa hukumar su kawo rasitansu musamman ga wadanda muka kai jaiz kuma suke da sha’awar tafiya a bana , wadanda Kuma basu da niyya kofarmu a bude take da su zo domin karbar kudaden su”. A cewar Abba Danbatta
Danbatta yace za’a fara jigilar alhazan Nigeria zuwa kasa Mai tsarki daga ranar 04 ga watan mayu na wannan shekara, yace hakan ce tasa a mako mai zuwa zasu tafi kasa Mai tsarki domin fara duba masaukan da zasu sauke alhazan