Tinubu ya ziyarci Sarkin Kano tare da neman addu’arsa

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da mutunta shugabanni, sannan su yi amfani da kuri’unsu wajen zaben shugabanni na gari a lokacin zabe .

 

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Apc, Asiwaju bola Ahmad tunibu a fadar sa.

Talla

Cikin sanarwar da sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24 yace Sarkin wanda ya bayyana Kano a matsayin cibiyar harkokin zabe ya yi kira ga jama’a da su yi amfani da kwarewarsu wajen zaben wadanda za su inganta rayuwar al’umma gaba daya.

 

Tun da farko dan takarar shugaban kasa Cif Bola Ahmad Tunibu ya ce ya zo jihar Kano ne domin kaddamar da yakin neman zabensa a Arewa maso Yamma kuma ya nemi addu’ar Sarkin da kuma al’ummar jihar.

Talla

 

A yayin ziyarar dan takarar shugaban kasa Bola Ahmad Tunibu ya samu rakiyar gwamnan jihar Dr. Abdullahi umar Ganduje, da mataimakinsa Dr. Nasiru yusif Gawuna, gwamnan jihar Zamfara, Sanata barau jibrin, shugaban jam’iyyar na jiha Abdullahi Abbas, tsofaffin gwamnoni, da manyan jami’an gwamnatin tarayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...