Daga Kamal Yakubu Ali
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya yi alkawarin bunkasa tsaro da harkokin tattalin arzikin jihar kano idan ya zama Shugaban Kasar Nigeria.
Bola Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da malaman Arewa maso yammacin Nigeria a jihar Kano.

Yace kasancewar kano cibiyar Arewacin Nigeria akwai bukatar a bata kulawa ta musamman saboda idan ta bunkasa dukkanin jihohin Arewacin Nigeria sun bunkasa.
Bola Tinubu ya kuma yi alkawarin samar da wani tsari da zai taimaka wajen inganta harkokin karatun al-qur’ani saboda magance matsalar barace-barace a kasar nan.
Ya kuma yi alkawarin baiwa malamai dama a gwamnatin tarayya ta yadda za’a dama da su domin inganta kasar nan. Tinubu ya bukaci Malamai da su umarci dalibansu da sauran magoya bayansu da su zabe shi saboda yafi dukkanin yan takarar shugaban kasa chanchanta.

Da yake nasa jawabin gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ƙalubalanci masu ganin baiken jam’iyyar APC don ta haɗa yan takarar shugaban kasa duk Musulmi, Inda yace haɗa Musulmi da Musulmi a takarar shugaban kasa ba sabon Abu bane a Ƙasar nan.
Ganduje ya kuma bada tabbacin cewa al’ummar Nigeria suna son jam’iyyar APC da yan takarar su Kuma zasu zabe su a babban zaben Mai zuwa .
Malamai da dama ne dai suka zo taron wadanda suka fito daga jihohin Arewacin Nigeria domin halartar taron wanda ke cikin jerin tarukan da aka tsara don yakin neman zaben Tinubu a kano.