Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi dan Majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Gwale HON. Yusuf Babangida da akafi sani da DAWO-DAWO wanda ya chanja sheka daga Jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar APC.
Hon. Yusuf Babangida dawo-dawo na cikin yan gaba-gaba a cikin darikar kwankwasiyya, da kuma adawa da gwamnatin Ganduje, amma yau yace ya fice daga jam’iyyar NNPP ya koma tafiyar jam’iyyar APC.

“Allah ya ganar dashi gaskiya ya bar Jam’iyyar NNPP bisa dalilan rashin adalci, rashin tsari da kuma rashin nasara da jam’iyyar ke fuskanta”. Dawo-Dawo
Cikin wasu jeren hotuna da S A Photography Aminu Dahiru ya wallafa sun nuna Gwamna Ganduje tare da Dan takarar mataimakin gwamnan Jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo da shugaban Jam’iyyar APC Alhaji Abdullahi Abbas wajen tarbar Sabon dan jam’iyyar.

Amma dai wasu suna ganin Dawo-Dawon ya fice daga jam’iyyar NNPP ne saboda ya rasa takarar Dan majalisar dokoki ta jiha Kano kujerar da yake kanta tun shekara ta 2011.