Kashim Shattima yace Tinubu ya fi shi lafiya

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mataimakin dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima, ya bayyana cewa mai gidansa, Bola Tinubu, ya fi shi lafiya.

 

Shettima ya bayyana haka ne a ranar Lahadi da daddare a wani shiri na kai-tsaye ta Facebook, mai taken “Fashin Baki”, wanda Bulama Bukarti, Nasir Zango, Abba Hikima da Jaafar Jaafar su ke shirya wa.

 

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa, ana nuna damuwa kan yanayin lafiyar dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, inda wasu ke cewa bai cancanci zama shugaban kasa ba.

Talla

Amma Shettima ya ce Tinubu ya ma fi shi lafiya domin ba shi da ciwon suga ko hawan jini.

 

“Bari in fada muku karara cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mutum lafiya garau ya ke. A ajiye siyasa a gefe, Tinubu na da lafiya a jiki da kuma karfin tunani da zai iya rike Nijeriya.

 

“Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fi ni koshin lafiya kasancewar ni ina da ciwon suga da hawan jini, wanda shi kuma ba shi da shi. Ko da ma cutar Parkinson da mutane suka yi magana game da ita, rashin barci ne kawai. Da zarar ya sami isasshen barci, zai zama ya yi garau.

Tallan Garin dan wake mai inganci

“Shugabanci ba kamar aikin ƙarfi na daukar buhunan siminti ba ne. Yawanci aiki da ƙwaƙwalwa ya fi yawa a kan da jiki. Tsofaffin shugabannin kasa, Theodore Roosevelt da Abdelaziz Bouteflika da Daniel arap Moi na Amurka da Aljeriya da Kenya sun jagoranci kasashensu ta hanyar bunkasar tattalin arziki yayin da suke kan keken guragu,” in ji Shettima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...