Nigeria na duba yiwuwar tallafawa ƙasar Burundi da Man fetur – Buhari

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ƙasar za ta duba buƙatar taimakon makamashi, musamman man fetur da gwamnatin ƙasar Burundi ta gabatar wa ƙasarsa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adeshina ya sanya wa hannu, shugaba Buhari ya yi alƙawarin ne bayan karɓar baƙuncin ministan kuɗi , kasafi da tsare-tsare na ƙasar Burundi Audace Niyonzima a fadarsa da ke Abuja.

Talla

Sanarwar ta ce Buhari ya tabbatar wa da mista Niyonzima cewa Najeriya za ta taimaka wa ƙasar Burundi ta hanyoyi da dama ƙarƙashin inuwar zumunci da ‘yan uwantaka da ke tsakanin ƙasashen Afirka.

Shugaba Buhari ya ƙara da cewa ya san yadda ƙasa ke ji musamman idan tana fama da ƙarancin makamashi, tare da alƙawarta cewa zai tura batun ga babban kamfanin mai na ƙasar NNPC domin duba buƙatar.

Talla

Buhari ya ce a yanzu batun zaɓen ƙasar, da batun saukarsa daga mulki ne a gabansa, tun da dai ya yi wa’adi biyu da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi dama.

A nasa ɓangare ministan na Burundi ya yi wa ƙasar fatan alkairi a manyan zaɓukan da za ta gudanar cikin wannan shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...