Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya bukaci al’ummar jihar da kada su zabi jam’iyya ko ‘yan takara da ba za su yi wa jihar aiyukan ci gaba ba a zaben 2023 mai zuwa.
Wike, a sakonsa na sabuwar shekara ta 2023 da aka rabawa manema labarai a Fatakwal a ranar Asabar, ya ce dole ne masu kada kuri’a a jihar su guje wa zabar wadanda suka gaza wajen ciyar da jihar gaba.

Gwamnan ya nanata cewa ba al’adar gwamnatin sa bace ta yi katsalandan ko tauye hakkin ‘yan siyasa da jam’iyyunsu na gudanar da yakin neman zabensu a fadin jihar.
Ya ce, “Amma dole ne a tunatar da mu cewa muna da dokoki da ka’idojin da suka hana yin harkokin siyasa a makarantun gwamnati da sauran wuraren zama domin dakile munanan dabi’u da hargitsin jama’a da galibi ke hade da irin wadannan abubuwan idan al’amura suka lalace.
