Daga Nazifi Bala Dukawa
Dan takarar majalisar wakilai mai Wakiltar birni a tutar jam’iyyar NNPP mai kayan marmari Hon Eng sagir ibrahim koki ya ce yana taya daukacin al’ummar Karamar hukumar birni dama kasa baki daya murna shigowa sabuwar Shekara ta 2023.
Dan takarar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24 a Kano.

Sagir koki Yana Kira ga al’umma da a cigaba da gabatar da adduo’i na musamman ga wannan kasa akan Allah ya bada zama lafiya Allah kuma yasa ayi zabe lafiya agama lafiya
“Ubangiji Yasa Wannan Shekara Ta Zama. shekarar Budi Da Kuma Daidaituwar al’amurra a wannan kasa Ameen”.

Yana kuma kara kira ga matasa da iyaye mata wajan zuwa su karfi Karin zabensu da ake bayarwa a hadin yanzu dakuma adanashi domin yanzu haka ansami wasu mutane Suna bi gida gida Suna karbe Karin iyayenmu mata
Alh Sagir Ibrahim koki ya kuma nuna farin cikinsa da irin addu’oin da aka Masa na fatan alkhairi da zaman koki Yana da kudurin samawa matasa aiki da mata da marayu da Kai kuduri a majalisa don haka ma kowace mazaba akayimata aikin bowel da koyawa matasa da mata 120 computer tare da biyawa yara kudin makaranta