Daga Aisha Aliyu Umar
Gwamnatin Tarayya, a ranar Juma’a ta ce ba wani shiri da take yi na karawa ma’aikatan ta Albashi kamar yadda aka ruwaito a wasu jaridun kasar nan suka rawaito kwanakin baya, inda ta ce wasu “alawus-alawus na musamman” ne kawai take shirin karawa .
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Olajide Oshundun ya fitar, inda ya jaddada cewa babu batun sake yiwa ma’aikata karin Albashi.

Ngige, yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata, ya ce kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan albashin ma’aikata na yin nazari, kuma ana sa ran zai fito da tsarin daidaita albashin a sabuwar shekara.

Sai dai ministan a ranar Juma’ar nan ya ce Ngige ya ce karin da ya yi magana a kai shi kan alawus din wasu ma’aikatan na musamman ba wai karin Albashi ba, inda ya kara da cewa har yanzu ana kan aiki.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kwamitin shugaban kasa kan albashi (PCS) ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya (OSGF) ya karbi shawarwarin duba alawus-alawus na ma’aikatu da hukumomin gwamnati da dama.