Ba abun da zai hana mu rushe gidaje akalla 1000 don inganta wutar lantarki a Kano – TCN

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

 

Kamfanin tunkudo hasken wutar lantarki na kasa, TCN, ya yi gargadin cewa babu gudu babu ja da baya kan shirin rusa gidaje sama da 1000 da aka yi su a karkashin wayoyin wutar lantarki a Kano domin sake gina layukan wutar lantarki daga Kaduna zuwa Kano.

 

Mataimakin Babban Manajan Kamfanin na TCN, Muhammad Kamaru Bello, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a kano.

 

Ya ce jihar kano na da layin daya tilo da ya ke kawo wutar lantarki daga Kaduna, kuma an kafa shi a cikin shekaru 50 da suka gabata.

 

“An gina tashar DanAgundi shekaru 50 da suka gabata akan karfin megawatt 80 amma a yau yana aiki fiye da megawatts 280 don haka ne ma muke son gudanar da aikin gaba daya domin samar da karin wutar lantarki ,” in ji shi.

Talla

Ya bayyana cewa an tauye musu mafi yawan hakkokinsu, kuma hakan ya biyo bayan biyan diyyar Naira biliyan 1.5 yayin da Kano ta biya Naira miliyan 500 na DanAgundi zuwa tashar Rimin Zakara.

 

Ya ce an kammala duk wasu aiyukan na bada kwangilar kuma nan da ’yan kwanaki masu zuwa za a fara aikin sake gina layukan wutar lantarki daga Kaduna zuwa kano, yana mai jaddada cewa ba za a ja da baya da aikin ba.

 

Tallan Garin dan wake mai inganci

Bello ya musanta cewa gidajen da aka ware domin rugujewa sun haura 20,000, inda yace daga DanAgundi zuwa tashar wutar lantarki ta Kumbosto gidaje da gine-ginen da ba a kammala ba da aikin zai shafa ba su wuce 1000 ba.

 

Ya kara da cewa, “yau a fadin Najeriya jihar Kano ce kadai ke fama da matsalar samar da wutar lantarki, kuma hakan ya faru ne saboda dukkanin layukan da ake da su sun tsufa kuma mutane sun yi gine-gine a kusa ko ma karkashin wayoyin wutar lantarkin .

 

“Bari in tunatar da masu dagewa cewa sai mun biya diyya kafin su bar wuraren na su, cewa TCN ba ta biyan diyya sau biyu, mun biya kafin mu Samar da tashoshin DanAgundi zuwa Rimin Zakara, Inda muka biya Naira biliyan 1.5 yayin da gwamnatin Kano ta biya Naira miliyan 500. to me suke magana akai?”.

 

Ya bayyana cewa ayyukan za su amfanar da jihohin Kano, Jigawa, Katsina, da wasu sassan na jihar Bauchi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...