Daga Aisha Aliyu Umar
Kwamandan Hukumar hisbah ta jihar Kano Sheikh Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya ce hukumar zata cigaba da aiki da Takwararta ta jihar Kaduna domin Dabbaka harkokin Addinin Musulunci.
Sheikh Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan a ziyarar aiki da ya kaiwa takwaransa a Kaduna.
Haroon Ibn Sina wanda mataimakinsa a bangaren horarwa Malam Idris ibn Umar ya wakilta ya ce babbar nasara ce da hukumar a jihar Kaduna ta samar da Dakarunta a Zaria da kewaye domin zai tallafa wajen yaki da Badala da kuma aikata bai dai-dai ba a jihar.

Ibn Umar ya ce kofar hukumar Hisbah ta jihar Kano a bude yake wajen neman shawara da goyon baya ko horarwa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Malam ibn Umar ya ce adadin sababbin dakarun su 75 a zazzau zai taimakawa hukumar kwarai da gaske wajen gudanar da ayyukan ta.