Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnatin jihar kano tace zata bude Sabuwar Tashar samar da wutar Lantarki mai Karfin Megawatts 10.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace anasa ran nan da mako 6 za ai bikin kadammar da Tashar da take Tiga.

Anasa ran tashar zata samar da wuta mai Karfin KV 33 ga Tashar Ruwa ta Tamburawa da Kuma Haskaka Titunan Jihar Kano.

Yayin da ya ziyarci Inda ake aikin wutar dake garin Tiga, Gwamna Ganduje yace ya gamsu da ingancin aikin da aka gudanar a wajen, Inda ya yabawa hukumar kula da wutar lantarki ta jihar kano bisa kokarin da suke don tabbatuwar aikin.
Tini dai gwamnatin jihar kano ta sanarwa da tashoshin wutar lantarkin lasisin fara aikin tun a watan Yuni na shekara ta 2021 daga hukuma dake bada lasisin don fara aiki gadan-gadan.

Ganduje ya bada tabbacin zai cigaba da gudanar da aiyukan da zasu inganta rayuwar al’ummar jihar kano gabanin karewar wa’adin mulkin sa, don barwa al’ummar Kano abun da zasu dade suna tunawa da shi .