Daga Kamal Yahaya Zakaria
Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) a karshen makon nan ya yi alkawarin kara yawan jami’an tsaron Najeriya da kashi 400 idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekarar 2023.
Kwankwaso wanda ya yi magana a Dutse, babban birnin jihar Jigawa ya bayyana cewa adadin jami’an tsaro a halin yanzu yayi kadan .
Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce “adadin ‘yan sandan Najeriya, sojoji, jami’an tsaron farin kaya da jami’an tsaron na civil defense da duk wasu jami’ai dake damara ba su da yawan da zasu magance matsalolin da tsaron da kasar nan take fuskanta”.

A cewarsa “idan aka yi la’akari da yawan al’ummar Najeriya kuma idan aka kwatanta da yawan jami’an tsaro, babu yadda za a yi su magance aikata laifuka da Najeriya”.
“In Allah ya yarda idan na zama shugaban Najeriya, zan ninka adadin ‘yan sanda, Sojoji, jami’an tsaron farin kaya DSS da dai sauransu da kashi 400 cikin 100”, in ji Kwankwaso.