Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Sadiq Wali, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano, ya sha alwashin zuwa kotun daukaka kara bayan wata babbar kotun tarayya da ke jihar ta kore shi.
Babbar kotun tarayyar ta bayyana Mohammed Sani Abacha, dan gidan marigayi shugaban kasa, Janar Sani Abacha, a matsayin zababben dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Kano ranar Alhamis.
Hukuncin, wanda Alkalin Kotun, Mai shari’a A.M Liman ya yanke, an yanke shi ne ta hanyar manhajar zoom, inda ya umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC da ta cire sunan Sadiq Wali tare da maye gurbinsa da na Muhammadu Abacha.

Daga nan ne kotun ta amince da zaben fidda gwani da bangaren Shehu Wada Sagagi suka gudanar a gidan Lugard, wanda ya fitar da Muhammad Abacha sabanin na wanda Akai a Abacha Youths center wanda ya samar da Sadiq wali.
Wanda bai gamsu da hukuncin ba, Sadiq Wali dan tsohon Ministan Harkokin kasashen Waje, Aminu Wali, ya ce zai garzaya kotun daukaka kara.
Da yake zantawa da manema labarai a Kano a yammacin ranar Alhamis, Wali ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar PDP da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa lauyoyinsa na nazarin “hukunce-hukuncen da akai, wanda suke zargin suna yana cike da tattare da kura-kurai” a kokarin su na shirye-shiryen daukaka kara.
A cewar Wali, tuni lauyoyinsa suka gano kura-kurai da dama kan hukuncin, wanda hakan zai bashi kwakkwarar hujjar maido da abin da ya bayyana a matsayin ‘yancin mutanen Kano a kotun daukaka kara.
Sadiq Wali ya bayyana cewa wani dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Ja’afar Sani Bello, ya maka shi kotu domin kalubalantar takararsa amma ya samu nasara a kotun daukaka kara.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa “zamu yi nasara a kotun daukaka kara in Allah ya yarda, za mu yi nasara kuma za mu yi nasara a zaben 2023 da yardar Allah.
“Wannan hukuncin yana cike da kurakurai amma saboda ni ba lauya ba ne, ba zan iya cewa komai kan wannan lamarin ba, amma lauyoyi na za su yi magana a kai,” in ji Wali.
A nasa bangaren, lauyan Sadiq Wali, Nasir Adamu Aliyu (SAN) ya ce sun tattara hujjoji sama da ashirin na kariya a kotun daukaka kara.
A cewar Aliyu, Wali ya samu nasara a kotun daukaka kara lokacin da Ja’afar Sani Bello ya shigar da kara yana kalubalantar zaben fidda gwani bayan da uwar jam’iyyar PDP ta sanya idanu.
- “Mun samu nasara a kotun daukaka kara a kan cewa duk wani zaben fidda gwani da jam’iyyar reshen jihar kano ta gudanar, ba na kasa ba, ba shi da tushe balle makama, kuma ba mu shiga cikin karar Ja’af din ba, amma babbar kotun ta dage. cewa dole ne mu shiga karar, daga karshe, mun yi nasara a kotun daukaka kara.
- “Kotun daukaka kara ta ce ba su da hujjar shigar da karar Sadiq Wali saboda zaben fidda gwani da suka gudanar ba wai jam’iyyar PDP ta kasa ce ta shirya shi ba, kuma uwar jam’iyyar ta kasa ce ta Sanya idanu kamar yadda doka ta tanada . ” Aliyu, SAN, ya bayyana.
Ya kara da cewa za a ba su kwafin hukuncin da aka yanke ranar Alhamis a shirye-shiryen su na daukaka kara.
Ya ce wani kuskuren da alkali ya yi shi ne, sanar da zaben fidda gwani ga hukumar zabe ta kasa INEC, ba hedikwatar ta ta jihar kano ba.
Dangane da wannan batu, Aliyu ya bayyana cewa sashe na 82 na dokar zabe ta 2022 ya ce a kai sakamakon zaben fidda gwani ga hedkwatar INEC ta kasa, ba jiha ba, cikin kasa da kwanaki 21.
Don haka lauyan ya bayyana cewa Wali ya ba shi damar shigar da kara a yau Juma’a.
Shi ma da yake nasa jawabin mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Kano, Dakta Yusuf Bello Dambatta ya ce jam’iyyar ta yi hasashen hukuncin tun kafin a zartar da shi.
A cewarsa, bangaren Wali bai ji dadin hukuncin ba saboda suna da kwararan dalilai na kalubalantar hukuncin a kotun daukaka kara.
Ya kuma bayyana fatansa na cewa ba za su huta ba har sai sun dawo da hakkinsu a kotun daukaka kara sannan su ci zabe domin yi wa al’ummar jihar hidima.
Daga nan sai Dambatta ya yi kira ga dimbin magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar da su kwantar da hankalinsu, ya kara da cewa hukuncin ba zai hana jam’iyyar ci gaba da ayyukanta ba.
Ya kara da cewa, suna shirye-shiryen kalubalantar hukuncin, tare da bayyana fatansu na samun nasara a kotun daukaka kara.