Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Dan takarar shugaban kasa a tutar jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa da zarar an zabe shi a zaben 2023 zai bada umarnin bude iyakokin kasar nan da gwamnatin APC ta rufe tun shekara ta 2015.
Kadaura24 ta rawaito Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar Katsina, lokacin da ya je jihar domin yakin neman zabe.
Yace an rufe iyakokin ne ba bisa ka’ida ba, shi yasa al’ummar jihar da wadanda suke makwabtaka da su suke cikin bakin talauci da sauran matsaloli na rashin tsaro.

- ” Duk mutumin da yake kasuwanci da jarin da bai Gaza Naira Miliyan 5 ba a jihar Katsina, an karya shi saboda Wannan tsarin da aka kawo, don haka ina baku tabbacin idan kuka zabe ni ranar da aka rantsar da ni washe gari zan bada umarnin bude duk iyakokin da suka rufe muku don cigaba da neman arziki”. Inji Atiku
Yace rufe iyakokin babu abun da ya haifarwa Yan Arewa face matsalolin rashin tsaro da talauci da Kuma da wahalar rayuwa.
Dama dai al’umma musamman yan arewacin Nigeria sun jima suna ta kiraye-kirayen gwamnatin tarayya ta bude iyakokin domin samun saukin matsalolin da al’umma suke ciki.