Daga Auwal Alhassan Kademi
Shugaban majalisar dokokin jihar Taraba, Farfesa Joseph Albasu Kunini ya yi murabus daga mukaminsa.
Politics Nigeria ta ruwaito cewa Farfesa Kunini ya bayyana dalilansa na kanshin kansa da suka sa ya yanke shawarar barin mukamin nasa.
An zabi Kunini kakakin majalisar ne a shekarar 2019 bayan murabus din tsohon shugaban majalisar, Abel Peter Diah ya yi tun a wancan lokaci.

Sanarwar murabus din Farfesan na kunshe ne a cikin wata wasika da aka aikewa βyan majalisar a ranar Laraba kuma mataimakin shugaban majalisar, Hammanadama Ibn-Abdullahi ya karanta yayin zaman majalisar .
βYan majalisar dai sun zabi John Kizito Bonzena, bulaliyar majalisar, wanda kuma shi ne yake wakiltar mazabar Zing, a matsayin sabon Shugaban majalisar.