Zan bude iyakokin kasar nan na Arewa kwana daya da rantsar da ni don maganin rashin tsaro – Atiku Abubakar

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Dan takarar shugaban kasa a tutar jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa da zarar an zabe shi a zaben 2023 zai bada umarnin bude iyakokin kasar nan da gwamnatin APC ta rufe tun shekara ta 2015.

Kadaura24 ta rawaito Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar Katsina, lokacin da ya je jihar domin yakin neman zabe.
Yace an rufe iyakokin ne ba bisa ka’ida ba, shi yasa al’ummar jihar da wadanda suke makwabtaka da su suke cikin bakin talauci da sauran matsaloli na rashin tsaro.
Talla
  • ” Duk mutumin da yake kasuwanci da jarin da bai Gaza Naira Miliyan 5 ba a jihar Katsina, an karya shi saboda Wannan tsarin da aka kawo, don haka ina baku tabbacin idan kuka zabe ni ranar da aka rantsar da ni washe gari zan bada umarnin bude duk iyakokin da suka rufe muku don cigaba da neman arziki”. Inji Atiku
Yace rufe iyakokin babu abun da ya haifarwa Yan Arewa face matsalolin rashin tsaro da talauci da Kuma da wahalar rayuwa.
Dama dai al’umma musamman yan arewacin Nigeria sun jima suna ta kiraye-kirayen gwamnatin tarayya ta bude iyakokin domin samun saukin matsalolin da al’umma suke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...