Daga Rukayya Abdullahi Maida
Wani masarake kuma dan kishin kasa Amb. Dr. Yunusa Yusuf Hamza Falakin Shinkafi ya yi kira ga al’ummar Nigeria da su guji sayar da kuri’unsu yayin babban zaben shekara 2023 dake tafe.
- “Babu shakka ana fama da talauci, amma bai kamata ya zama dalilin da zai sa al’ummar Nigeria su sayar da kuri’unsu ga gurbatattun shugabanni ba”. Inji Falakin Shinkafi
Amb. Dr. Yunusa Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da shirin Demokaradiyya adon kasa na gidan Radion Nigeria Kaduna.

Yace duk da irin matakan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dauka domin dagile magudin zabe a bana, Amma har yanzu wasu yan siyasar sun tara magudan kuɗade domin baiwa talakawa don su zabe su.
Falakin Shinkafi wanda ya shahara wajen tallafawa matasa yace kamata yayi yan Nigeria su dubi chanchanta lokaci zabe, saboda zabar Shugaba nagari shi ne zai sa a sami saukin tarin matsalolin da ake fuskanta a kasar nan.
- ” Duk wanda zai baka kudi don ka zabe shi to ka sani idan yaci zaben sai ya mayar da kudaden daya baku idan ma zai yi muku wani abun kirki, Amma idan chanchanta kuka bi to wlh kun tsira har a gurin Allah”.
” Ni a Sani na ban taba ganin an sayi kuri’u da kudin da suka taka Kara suka karya ba, a baka dubu da Kuma kaje asibiti ko ka kai matarka ko ‘ya’yanka ka kashe sama da gubu 50 me gari ya waya, kuma kaje ka fadawa Allah dalilin da yasa ka yi haka”. Inji Falakin Shinkafi
Daga ƙarshe yayi fatan Samun shugabanni nagari wadanda zasu taimaka wajen fitar da al’ummar Nigeria daga cikin mawuyacin halin da suke ciki.