Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar gudanarwar Gidan rediyon Premier ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa wani ma’aikatanta, mai suna Muhammad Bello Dabai a bakin gidan Radiyon tashar yayin da yake gudanar da aikinsa a ranar Litinin da yamma.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban Sashin labarai na gidan radion Premier Mukhtar Yahaya Usman ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Wannan mummunan lamari dai ya faru ne da misalin karfe 3:30 na rana inda aka kira hankalin Muhammad Beelo Dabai domin ganewa idanunsa wani barawon da ya tsere wanda mutane suka biyo shi bayan da ya gudun hdaga Asibitin Nassarawa inda ‘yan sanda suka kai shi asibitin domin yi masa magani.

Yayin da jama’a ke bin sa suna jifansa da duwatsu, sai barawon ya fadi a gaban Radiyon, “Inda Ma’aikatanmu da suka hada da Muhammad Bello Dabai suka fito don ganewa idonsu abun dake faruwa, Kuma lamarin ya faru ne a gaban dan sanda da ke kula da ofishinmu, wanda ya kirawo Area Command don su kawo dauki .
A lokacin da ‘yan sandan suka isa wurin domin daukar mai laifin, a dai-dai lokacin Dabai yana daukar lamarin ne a matsayinsa na dan jarida. Wani abin mamaki shi ne yadda wani daga cikin ‘yan sandan ya tunkare shi domin ya hana shi, sai dai Dabai ya nuna masa katin shaidarsa, kuma ya bayyana kansa a matsayin dan jarida, amma dan sandan ya kama shi da karfin tsiya ya tura shi cikin motar su, inda ya bayyana cewa za su kai shi ofishin ‘yan sanda domin yi masa tambayoyi tare da tsare shi.
Sanarwar tace dan sandan ya yiwa Dabai dukan tsiya tare da marin sa tun suna kan hanyarsu ta zuwa ofis, inda kuma aka tilasta masa ya kwanta a budadden sashin motar.
Yayin da gidan rediyon Premier cikin gaggawa ya kai rahoton lamarin ga kwamandan rundunar ‘yan sandan yankin domin a sako ma’aikacin nasu, kwamandan yankin ya tsawatar wa jami’an nasa kan abun da sukai, sai dai jami’an ‘yan sandan basu nuna nada akan abun da suka yi ba.
“Muna bukatar a dauki kwararan matakai a kan wadannan jami’an da ba su yi nadamar cin zarafin ma’aikacin mu ba, sannan dole ne su neman afuwar abun da suka ba tare da kawo wani uzuri ba, wanda idan ba haka ba, muna da ‘yancin neman hakkin mu a gaban shari’a”.