Wata Musulma a Kaduna ta raba kayan abinci, atamfofi da kuɗi ga mata kiristoci 50 

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

 

A wani bangare na bikin Kirsimeti na bana, wanda ya zo a cikin tashin farashin kayayyaki, a fadin kasar, wata mata musulma, Ramatu Tijjani, ta sake raba kayan abinci da zannuwa da kuma kyautar kudi ga zawarawa Kiristoci 50 a jihar Kaduna.

 

A cewarta, ta ƙissima za ta raba wa zawarawa sama da 200, tana mai cewa hakan wani bangare ne na kokarin inganta zaman lafiya a tsakanin addinai daban-daban.

 

Ta ce an bayar da kyaututtukan ne da nufin sanya musu farin ciki a fuskarsu ta yadda za su kula da marayun su da kuma ba su damar gudanar da bukukuwan cikin farin ciki da jin dadi kamar sauran Kiristocin duniya.

 

Talla

Tijjani ta bayar da gudummawar ne a cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, Sabon Tasha, a jiya Lahadi a Kaduna.

 

A cewarta, gudummawar ta samo asali ne daga sha’awarta da kuma buƙatar yin tasiri ga rayuwar zawarawa marasa galihu waɗanda suka sha wahala da wariya har ma sun fara fitar da rai da rayuwa.

 

Ta ce tun shekaru 10 da suka gabata, tana bayar da gudummawar buhunan hatsi, kayan sawa da lemukan sha ga zawarawa Kiristoci da marayu a lokacin Kirsimeti, da bukukuwan Ista da nufin karfafa dangantakar Kiristoci da Musulmi a yankin Arewa.

 

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, matan kiristocin sun kira Tijjani da “Mama” ne saboda kyakkyawar alaka da ta kulla da su wajen karfafa alaka tsakanin Kirista da Musulmi a jihar da ma kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...