Mutum 12 sun rasa rayukansu a hadarin mota a hanyar Neja

Date:

Rahotanni sun ce a kalla mutane 12 sun rasa ransu bayan da wasu manyan motoci biyu makare da waken suya da kantu suka yi taho mu gama a hanyar Lambata zuwa Agaie zuwa Bida.

 

Shugaban hukumar kiyaye afkuwar hadura a jihar Neja, Kumar Tsukwam, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce hadarin ya afku ne a ranar Asabar da misalin karfe biyar na safe.

 

Ya ce bayan afkuwar hadarin ta ke mutum 12 suka rasa ransu, yayin da wasu 10 kuma suka samu raunuka kuma tuni aka kai su zuwa asibitin Agaie don duba lafiyarsu.

Talla

BBC Hausa ta rawaito Tsukwam, ya ce manyan motocin da suka yi hadarin na dauke da mutane 75 wadanda suka nufi jihar Legas daga arewa.

 

Ya kuma danganta afkuwar irin wadannan hadurra da gudun wuce kima da kuma rashin kiyaye dokokin hanya.

 

Daga nan ya ba wa masu ababan hawa shawara a kan su rinka takaita gudu da kuma kula da kiyaye ka’aidojin tuki da hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...