Daga Yakubu Abubakar Gwagwarwa
Zunzurutun yan boko a yankin kura madobi da garun Mallam sun bayyana goyon bayan su ga dan takarar majalisar tarayya na jam’iyyar APC Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso a zaben shakara ta 2023 dake tafe.
Shugaban gamayyar kungiyoyin dalibai da sauran yan bokon dake yankin Kwamaret Mukhtar, ne ya bayyana hakan yayin wani taron nuna goyon baya ga Musa Iliyasu Kwankwaso, wanda ya gudana a dakin taro na Sani Abacha Youths center a kano.
Kwamaret Mukhtar yace zasu goyawa Musa Iliyasu Kwankwaso baya ne saboda yadda a baya ya rika tallafawa daliban yankin da kudin tallafin karatun da sauran tallafi kan abun da ya shafi karatun su.
” Wannan kungiyar ta zunzurutun yan boko ce dake kura madobi da garun Mallam, mun yanke shawarar marawa Musa Iliyasu bayan ne saboda duk wani dan boko yaci Arzikin musa, ko kai tsare ko kuma ba ta kai tsaye ba, don haka muka ga dacewar Saka alkhairi da alkhairi”.

” Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso wadannan matasa da kake gani wakilcin kawai suka zo don jaddada goyon bayan mu ga takarar ka saboda muna da kyakyawan yaƙinin idan Allah ya baka wanann damar zaka tallafawa harkokin ilimi da sauran fannoni a yankin mu”. Inji Kwamaret Mukhtar
Shugaban gamayyar kungiyoyin ya Sha alwashin zasu koma mazabun su domin cigaba da wayar da kan al’umma maza da matasa muhimmancin zabar Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin dan majalisar tarayya, da Kuma irin alfanun da kowa zai samu idan Musa Iliyasu yaje majalisar.