Ɗan Nijeriya da ya je Saudiyya a keke ya faɗi yadda ya hadu da ƴan Boko Haram da ƴan fashin daji

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Jakadan Najeriya a Saudiyya Yahaya Lawal, ya tarbi Aliyu Bala, ɗan Najeriya da ya yi bulaguro a kan keke daga Jos a Jihar Plateau zuwa kasar Saudi Arabia.

Wata sanarwa da ofishin jakadanci da ke Jeddah ya bayar ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ta ce an baiwa Bala duk wani taimako da kwarin gwiwa da ake bukata na ofishin jakadancin.
Bala, wanda ya bar Jos a watan Fabrairun 2022 don gudanar da aikin Umrah a Makkah kuma ya ziyarci Masallacin Manzon Allah a Madina, ya isa ƙasar ne a ranar 8 ga watan Disamba.
Bayan ya gana da Jakadan, ya zarce zuwa Makkah inda ya yi Umrah, kuma zai yi kwanaki don yin ibada a dakin Ka’aba.
Talla
Bala, wanda shi ne na farko da ya fara gudanar da irin wannan tafiya daga Najeriya a wannan zamani, ana sa ran zai ci gaba da tafiyar kilomita 450 zuwa Madina inda ofishin jakadancin ya kuma shirya masa liyafar tarba.
Tun zuwansa Masarautar Bala ya kasance cikin lafiya da karsashi, bayan ya tsallake haɗarurruka iri-iri a tafiyarsa domin cimma burinsa na rayuwa.
Sai da ya ratsa kasashen Nijar da Chadi da Sudan kafin ya isa kasar Saudiyya.
Bala ya ce ya gamu da kalubale da dama a yayin tafiyar da suka hada da tsallake barazanar mayakan Boko Haram, masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi, da namun daji.
Ya ce ‘yan Boko Haram da ya gamu da su sun nemi ya yi musu addu’a, yayin da ‘yan fashin daji da ya hadu da su suka ƙwace masa wayar salula.
Sai dai da ya isa wani karamin gari a kasar Sudan, ya ba da labarin yadda ya sha fama da miyagun mutane, shi ne mutanen da ya hadu da su su ka taimaka masa, suka sayo masa sabuwar waya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...