Mai martaba Sarkin birnin gwari dake jihar Kaduna Malam Zubairu Jibril Mai Gwari II, ya nada dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu a matsayin dakaren birnin Gwari.

An dai gudanar da bikin nadin ne a jiya litinin a fadar Masarautar ta birnin gwari.
Al’umma da dama ne dai daga ko’ina a fadin kasar nan suka sami halartar bikin nadin wadanda suka hadar da yan siyasa gwamnoni, jami’an gwamnati, yan kasuwa da dai sauran al’umma.
Ga wasu daga cikin hotunan yadda akai nadin: