Mahukunta a Najeriya sun ce daga yanzu matafiya sun dai na nuna sakamakon basa dauke da cutar korona idan sun isa ko kuma za su yi tafiya zuwa wata kasa.
Hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta kasar ta ce an dauki matakin hakan ne bayan tabbatar da cewa a yanzu ba kasafai ake samun wadanda suka kamu da cutar ba a kasar dama sauran kasashen duniya.

Hukumar ta ce daga yanzu duk wani matafiyi daga gida Najeriya da ma wadanda suka dawo daga wata kasar ba za a bukaci sakamakon gwajin cutar da ya nuna basa dauke da ita ba.
A baya dai wajibi ne ga duk matafiya suyi gwajin cutar kafin tafiya, haka ma wadanda suka dawo dole su nuna sakamakon gwajin da ya nuna basa dauke da ita.