Buhari zai tafi Amuruka don halartar taron shugabannin Africa

Date:

 

Shugaba Muhammadu Buhari a gobe Lahadi zai tafi Amurka domin halartar taron shugabannin ƙasashen Afirka da Amurka za ta karbi bakunci.

 

A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kan kafofin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar yau Asabar, ya ce taron wanda za a gudanar daga ranar 13 zuwa 15 ga watan Disamba da shugaba Biden zai jagoranta, na da zimmar ganin ta yi aiki da gwamnatocin Afirka da kuma al’ummomin su da ke zama a ƙasar domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Amurka da ƙasashen Afirka.

 

Talla

Ya kara da cewa taron na kara neman karin hanyoyin da za a bi don inganta huldar tattalin arziki da samar da zaman lafiya da tsaro da kuma shugabanci na gari.

 

Gwamnonin jihohin Bauchi da Kwara da kuma wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati ne za su yi wa shugaban rakiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...