Kaiyade kudade: sabon tsarin CBN karya Kasuwanci zai yi a Nigeria – Kungiyar Masu fataucin Shanu

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

 

 

Shugabancin kungiyar masu fataucin shanu da dabbobi ta kasa ya koka dangane da ka’idojin da babban bankin kasar nan ya samar na takaita yawan kudaden da za’a fitar a bankuna, da cewa hakan zai durkusar da kasuwancin yayanta a Nigeria.

 

 

Shugaban kungiyar Alhaji Mustafa Ali ne ya sanar da hakan a zantawarta da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.

 

 

Mustafa Ali ya koka da cewar kamata yayi gwamnatin tarayya ta samar da tsarin da zai ceci yan kasuwa musamman kanana, kafin ta aiwatar da wannan sabon tsarin na sauya fasalin kudi ta yadda zai bunkasa tattalin arzikin kasuwanci a kasar nan.

Talla

 

Ya kuma koka dangane da yadda tsarin kasuwacinsu zai fuskanci kalubale idan har babban bankin kasa ya dage akan wadannan sabbin tsare-tsare da ya bijiro dasu na cewa mutum daya ba zai cire kudin daya haura naira dubu dari ba daga cikin asusun ajiyarsa na banki ba.

 

 

Shugaban ya bayyana cewa kasarnan ba ta kai munzalin da za tayi amfani da wannan sabon tsarin da ake yiwa lakabi da cashless policy ba, kasancewar tsarin tattalin arzikin kasar na cikin mashashshara.

 

 

Don haka ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan ta gaggauta yin duba na tsanaki kan wannan sabon tsarin da ba zai haifar wa da kasar nan da mai ido ba, wanda idan gwamnati bata farga ba zai lalata kasuwancin dubunnan al’umma a fadin kasar nan.

 

 

Daga karshe ya yi kira ga ya’yan kungiyarsu da su cigaba da baiwa Shugabancin kungiyar hadin kai da goyon baya kasancewar kungiyar a shirye take wajen kare musu mutuncinsu, da kuma kwatar musu yancinsu musamman wadanda ke gudanar da kasuwacinsu a sassa daban-daban na jihohin kudancin Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...