Daga Maryam Ibrahim zawaciki
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano karkashin jagorancin mai shari’a A.A Liman a ranar Larabar nan ta yi watsi da karar da hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya shigar gabanta,Inda ya ke kalubalantar nasarar Abdullahi Mahmud Gaya a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na mazabar Gaya/Ajingi/Albasu. a ranar 25 ga Mayu, 2022.
A cikin hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Liman ya ce mai karar ya kasa tabbatar da zargin dangwale kuri’un ga wadanda basu ya kamata su yi zaben ba, wanda yace an hana wakilansa 85 ‘yancin shiga wurin zaben.
Hakazalika kotun ta ce wanda ya yi zargin dole ne ya bayar da gamshashiyar hujja ba tare da kokwanto ba, yana mai jaddada cewa wanda ya shigar da karar ya gaza sauke nauyin da ke kan sa a matsayinsa na mai kara.

Idan dai za a iya tunawa Abdullahi Mahmud Gaya ya samu nasara ne da kuri’u 109 a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a mazabar dan majalisar wakilai da zai wakilci kananan hukumomin Gaya/Ajingi/Albasu .
Ahmad ya bayyana rashin gamsuwa da sakamakon, inda ya garzaya kotu yana rokon ta soke zaben tare da ba da umarnin sake gudanar da sabon zabe ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, sai dai a hukuncin da ya yanke mai shari’a Liman ya ce an gudanar da zaben ne daidai da tanade-tanaden Dokar zabe ta 2022 kamar yadda akai mata gyara.
Barista Abubakar Muhammad daga Nuraini Jimoh Law Firm ya godewa kotun da ta yanke hukuncin da ya dace.
A nasa bangaren, lauyan Bashir Ahmad, Barista Lawan Idris ya ce za su daukaka hukuncin a kotun daukaka kara.